Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Zamfara:Al’ummar kauyen Dan Jibga sun kashe yan bindiga 59 da suka kai musu hari

Published

on

Al’ummar garin kauyen Dan Jibga da ke yankin karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, sun kashe ‘yan bindiga hamsin da tara wadanda suka kawo hari kauyen nasu.

Haka zalika bakwai daga cikin al’ummar kauyen sun rasa rayukansu sakamakon batakashin da ya dau tsawon a wanni hudu ana fafatawa.

Rahotanni sun ce a shekaran jiya Talata ne ‘yan bindigar wadanda yawansu ya kai dari da tamanin suka isa kauyen na Dan Jibga dauke da manyan makamai lamarin da ya sa al’ummar kauyen wadanda ke cikin shirin kota kwana suka debo makamai domin kare kansu wanda a sanadiyar hakan suka kashe ‘yan bindigar hamsin da tara.

Wasu shaidun gani da ido sun ce tuni kwambar motocin sojoji suka isa kauyen sannan suka kafa sansani domin shirin tunkarar ko da ‘yan bindigar da suka tsira da rayukansu ka iya dawowa domin daukar fansa.

Mukaddashin mai magana da yawun rundunar sojin kasar nan manjo Clement Abiade, ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce, tuni sojoji suka bazama a dazukan da ke yankin domin gano ‘yan bindigar da suka tsere da raunuka a jikinsu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!