Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

KannyWood

Kamata ya yi gwamnatin tarayya ta samar da dokar sanya finai-finan Hausa a kowacce jiha – Jarumar Kannywood Mansurah Isa

Published

on

Tsohuwar Jarumar Kannywood Mansurah Isa ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su samar da dokar sanya finai-finan Hausa a kowacce jiha a faɗin kasar nan.

Jaruma Mansurah Isah ta bayyana hakane biyo bayan yadda aka iyakance fina-finan Hausa wajen tsallakawa da su zuwa sinimomin kallo na kudancin kasar nan.

Mansurah ta bayyana hakan ta cikin wani faifen bidiyo da ta wallafa a shafinta na sada zumunta na (Instagram) a ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Kazalika tsohuwar jarumar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba yanayin dokar dake kula da sahalewar haska fina-fanai a fadin kasar nan, duk da kuwa suma masu yin Hausa fim sun cancanci a basu damar haska fasahar tasu a faɗin kasar baki daya.

Mansurah ta ci gaba da faɗin cewa “masu shirya fim din Hausa suma ya kamata a kallesu tare da haska fina-finansu a ko ina acikin ƙasar”.

Haka kuma “na kalli yadda aka sahalewa fina-finan Nollywood, Bollywood, Hollywood nuna fina-finan dukkaninsu a fadin kasar nan saɓanin na Hausa”.

“mai yasa mu Kannywood hukumar dake kula da hakan ba za ta yi wani abu akan mu ba, mai muka yi muku? a cewar jarumar.

“Duk da cewa muna cikin masu taimaka muku wajan harkokin zabe da sauran al’amuran siyasarku kafin da bayan kakar siyasa amma kun barmu haka”

“Kowanne fim ba abin yarwa ba ne musamman Hausa fim a Najeriya, don haka ya kamata a sake duba wannan batu”.

Jarumar dai na wannan furuci ne adaidai lokacin da ta ke ci gaba da bada gudunmawa a masana’antar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!