Labarai
Ya kamata Gwamnatin Kano ta sanya ido kan harkar Noma- Abdullahi Idris
Shirin bunkasa harka Noma da kawar da yunwa a Najeriya ya bayyana cewa kamata ya yi gwmanatin kasar ta mai da hankali wajen inganta harkokin noma.
Shugaban shirin a jihar Kano Abdullahi Idris ne ya bayyana haka yayin bikin ranar manoma da ya gudana a garin Kadawa dake Kamar hukumar Garun Malam.
Abdullahi Idris ya kara da cewa kowane Dan Adam na bukatar nau’in abinci iri uku tun daga yarintarsa har zuwa girmansa.
Wanda hakan ne yasa shirin na Havest Plus ya dakufa domin samar da irin jan masara ,gero masu sinadari iron duba da mahimmanci sa a jikin Dan Adam.
Ya Kara da cewa Shirin ya Kuma samar da sabbin hanyoyin shuka abinci Mai gina jiki, dama hanyoyin sarrafasu a cikin gidajen, zuwa nau’ika daban-daban.
You must be logged in to post a comment Login