Labarai
Kamfanin jiragen sama na Air Peace zai kwashe ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan kyauta
- Kamfanin jiragen sama mai zaman kansa na Air Peace a Nigeriya ya bayyana shirinsa na kwashe ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan kyauta
- Kamfanin ya dauki matakin ne ganin cewa daliban Najeriya da ke Sudan na bukatar taimakon.
Kamfanin jiragen sama mai zaman kansa na Air Peace a Nigeriya ya bayyana shirinsa na kwashe ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan kyauta, matukar gwamnatin tarayya za ta iya ba su filin jirgin sama mai aminci da tsaro a duk wasu kasashen da ke makwabtaka da Sudan.
Hakan na cikin wata sanarwa da shugaban kamfanin kuma babban jami’in gudanarwa na kamfanin Allen Onyema ya fitar a yau litinin.
A cewar kamfanin, ya dauki matakin yin hakan ne lura cewa daliban Najeriya da sauran wadanda suka makale a kasar Sudan da ke fama da yaki suna bukatar taimakon cikin gaggawa.
Cikin sanarwar, Onyema ya kuma ce, ya zama dole ya taimaka domin Najeriya ba za ta iya rasa ‘yan kasarta a wata kasa da ke fama da yaki ba.
Idan za a iya tunawa ko a shekarar 2019, kamfanin na Air Peace ya tura jiragen sama don kwashe ‘yan Najeriya a Afirka ta Kudu, lokacin da kasar ke fama da rikicin kyamar baki, wanda hakan ya jefa barazana ga rayuwar ‘yan Najeriya da ke zaune a can.
Rahoton: Madeena Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login