Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An sahale wa jiragen Nijeriya tashi daga Masar don dauko daliban Sudan

Published

on

  • Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta fara jigilar dakko dalibai dama sauran ‘yan kasar da suka makale sakamakon yakin da ya barke a Sudan.
  • Ci gaban na zuwa ne ta cikin sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen da ma’aikatar jin kai da kiyaye afkuwar bala’o’I suka fitar.
  • A cewar gwamnatin tarayya hukumomin Najeriyar da ke Masar na ci gaba da tattaunawa da mahukuntan Masar don kwaso daliban.

Gwamnatin Najeriya ta ce jirgin Air Force C-130H, da na Air Peace da karin wasu kamfanonin jigila sun samu sahalewar tashi daga, Masar domin dauko ‘yan kasar da suka makale sakamakon yakin da ya barke a Sudan.

Wannan ci gaban dai na zuwa ne ta cikin sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar nan hadin gwiwa da ma’aikatar jin kai da kiyaye afkuwar bala’o’I ta kasa suka fitar a daren jiya alhamis, kan halin da ake ciki game shirin kwaso su zuwa gida Najeriya.

Haka zalika gwamnatin tarayyar ta ce hukumomin Najeriyar dake Masar na cigaba da tattaunawa da mahukuntan Masar din, kan shirin kwaso su, da samar musu da izinin gaggawa na shiga kasar, da kuma wajen zama zuwa lokacin da zasu taso zuwa gida Najeriya.

Rahoton: Ahmad Kabo Idris

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!