Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kamfanin NNPC yace batun daukar ma’aikata da ake yadawa ba gaskiya bane

Published

on

Kamfanin Man Fetur na Kasa NNPC ya bukaci jama’a su yi watsi da labaran da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa kamfanin yana daukar ma’aikata.

Kamfanin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi mai dauke da sa hannun mai magana da yawun sa, Garba Deen Muhammad, a Abuja.

Sanarwar ta kara da cewa duk lokacin da kamfanin ya yanke shawarar daukar ma’aikata, zai sanar da hakan ga jama’a ta ingantattun hanyoyin yada labarai, da kuma shafin kamfanin na NNPC wato www.nnpcgroup.com.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!