Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar ‘Yan-sandan Zamfara ta kama ‘Yan leƙen asiri 48 a watan Satumba

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta samu nasarar kama mutane 21 da ake zargin ‘yan-bindiga ne tare da ‘yan liken asiri 48 a watan Satumbar da ya gabata.

Mai magana da yawun rundunar SP Muhammed Shehu, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana ranar lahadi a Gusau, kan nasarorin da rundunar ta samu a wata guda.

Yace ‘yan bindiga 5 da sunayensu ke jerin wadanda ake nema ruwa a jallo sun mutu yayin wani sumame da rundunra ta kai.

Kazalika ya yi kira ga mazauna yankin da su yi hakuri tare da bai wa hukumomin tsaro goyon bayan da ake bukata don kawar da duk masu aikata laifuka da dawo da doka da oda.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!