Kiwon Lafiya
Kananan yara miliyan 821 ne basa samun isashshan abinci-kungiyar dalibai
Kimanin yara miliyan 821 ne basa samun isasshen abinci a Duniya sakamakon rashin wayewar bayar da abinci da ya kamata.
Shugaban kungiyar dalibai masu karantar lafiyar abinci na jami’ar Bayero ta Kano Auwalu Musa Umar, ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da Hantsi na Freedom Radio a safiyar Litinin 23 ga watan Satumba.
Auwalu Musa Umar ya ce daga cikin abubuwan da mata masu dauke da juna biyu ke mantawa shi ne irin abincin da ya kamata su ci lokacin da suke dauke da juna biyu.
Auwalu Musa Umar ya kara da cewa idan har mata bayan haihuwa za su rika shayar da yara yadda ya kamata to za a magance mutuwar jarirai miliyan 52 a Duniya.
Sannan kungiyar daliban masu karantar harkokin lafiyar abinci ta kuma gargadi mata da kada su bar yara kanana suna kwanciya da yunwa wanda hakan yake tasgaro ga lafiyar su.
Rahoto :Abbas Yushau Yusuf