Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: Ƴan sanda sun kama matasan da ake zargi da kashe abokinsu, dalibin Jami’ar Wudil

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane 2 wadanda ake zargi suna da hannu wajen kashe wani dalibin jami’ar kimiyya da fasaha ta Kano da ke garin Wudil.

 

Mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa shine ya tabbatar da wannan lamari yayin zantawa da wakilin mu Abdulkarim Muhammed Tukuntawa ta wayar tarho.

 

Ya ce an samu gawarsa a wani wajen tonon kasa da ke unguwar Mariri, inda bayan an gudanar da binciken farko ne kuma ‘yan sanda suka kama wasu abokansa biyu.

 

A baya-bayan nan ne dai aka tsinci gawar dalibin da ke karatu a jami’ar kimiyya da fasaha ta Kano da ke garin Wudil mai suna Ahmad Abubakar dan shekaru 22, kwanaki biyar bayan sanar da batarsa a makarantar.

 

Tun farko dai dalibin wanda ke shekara ta uku a sashen nazarin Physics a jami’ar ta Wudil kuma mazaunin birnin tarayya Abuja, ya bata ne a ranar asabar lokacin da ya fita zuwa kasuwar sayar da wayoyin hannu ta farm center don sayan waya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!