Labarai
Kano: Ƴan sanda sun kama matasa 21 bisa yunkurin tayar da tarzoma yayin Maukibi

Rundunar ƴan Sandan Jihar Kano ta ce, ta kama mutum 21 da ake zargi da yunkurin tayar da tarzoma yayin bikin Maukibi da aka gudanar cikin lumana.
Jami’an tsaro sun gano makamai masu hatsari da miyagun ƙwayoyi daga hannunsu, abin da ya taimaka wajen kare rayuka da tabbatar da tsaro.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta rawaito Kwamishinan ƴan Sanda, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce, wannan nasara ta samo asali ne daga dabarun tsaro na zamani da haɗin gwiwa da sauran hukumomi da shugabannin al’umma ke bayarwa.
Ya kuma yaba da yadda jama’a suka gudanar da bikin cikin kwanciyar hankali.
Haka kuma, rundunar, ta buƙaci al’umma da su ci gaba da ba da hadin kai ga rundunar yan sanda ta hanyar sanar da duk wani motsi ko mutum da ake zargi domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
You must be logged in to post a comment Login