Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: An kama wani mai kwacen waya da ya caka wa wata matar aure, karfe

Published

on

Wani matashi da ake zargi da addabar al’ummar Unguwar Ja’oji a nan Kano da sace-sace a gidaje ya shiga hannun hukuma bayan da aka kama shi yana cakawa wata mata sukundireba lokacin da yake kokarin kwace mata waya.

A cewar wakilin Freedom Radio Umar Abdullahi Sheka, matashin mazaunin unguwar ta Sheka mai suna Muhammad Isah da aka fi sani da Gunki, ya jima yana addabar al’ummar yankin da bin gidajensu yana sace-sace.

Ya kuma bayyana wa Freedom Radio yadda aka yi har ya shiga gidan matar tare da caccaka mata karfe.

”Gaskiya ne nine na caka mata sukundireba kuma nayi hakan ne da nufi sace mata waya, amma nayi nadamar wannan ta’addanci da na yi” a cewar Muhammad Isah (Gunki).

Ita ma matar wadda ba ta amince a bayyana sunanta ba, ta ce, tana kwance a daki ne kawai sai taga mutum akanta da farko ta yi zaton cewa danta ne amma daga bisani sai ta fuskanci cewa ba shi bane, lamarin da ya sa ba tare da bata lokaci ba, ta cakume kafarsa, inda nan ne kuma ya zaro sukundireba a aljihunsa ya rika caccaka mata.

Mutanen unguwar dai sun yi kira ga hukumomin tsaro da su kara karfafa matakan tsaro a cikin al’umma don magance ayyukan bata-gari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!