Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ngige: Zan dauki matakin shari’a kan gwamnonin da su ka rage albashin ma’aikata

Published

on

Ministan kwadago da samar da aikin yi, Sanata Chris Ngige, ya ce, tuni ya fara tuntubar atoni janar na kasa kuma ministan shari’a Abubakar Malami don neman shawararsa kan daukar tsastsauran mataki kan jihohi wadanda suke tattauna batun mafi karancin albashi da kungiyoyin kwadago na jihohinsu.

 

A cewar sanata Chris Ngige, lamarin zai iya kaiwa ya dauki matakin shari’a kan gwamnoni da kwamishinoninsu na kudi da kuma sauran jami’an gwmanati da suka shiga cikin harkokin neman ragewa ma’aikata mafi karancin albashin.

 

Ministan kwadagon ya bayyana hakan ne yayin zantawa da gidan talabijin na Channels.

 

Tun farko dai gamayyar kungiyoyin kwadagon sun bukaci gwamnatin jihohi da su guji ragewa ma’aikata mafi karancin albashin na naira dubu talatin wanda aka yi yarjejeniya aka  amince.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!