Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: An sako mahaifiyar ɗan majalisa bayan an biya kuɗin fansa

Published

on

Masu garkuwa da mutane sun sako mahaifiyar shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano Isyaku Ali Ɗanja.

Ɗan majalisar ne ya tabbatarwa da Freedom Radio hakan da safiyar Talata.

Ya ce, an same ta a garin Gumel na jihar Jigawa kuma yanzu haka suna kan hanya domin ɗaukota.

Wasu rahotanni sun ce kafin sakinta dai da aka biya kuɗin fansa kimanin Naira Miliyan Arba’in.

A ranar 12 ga watan Janairun da muke ciki ne, ƴan bindiga suka kutsa kai kai har cikin gidanta a garin Ɗanja na ƙaramar hukumar Gezawa, inda suka yi awon gaba da ita.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!