ilimi
Kano: An samar da sabbin makarantun kiwon lafiya a wajen birnin Kano
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, ta ce samar da makarantun koyar da kiwon lafiya a ƙananan hukumomin da ke wajen birni, zai taimakawa mazauna karkara damar samun ilimin kiwon lafiya.
Mataimakin shugaban kwamitin da Gwamnatin Kano ta kafa, Dakta Ashiru Rajab ne ya bayyana haka a ranar Litinin, yayin da ziyarci wuraren don duba yanayin kayan aiki, da gine-gine a makarantun lafiyar da aka samar a jihar.
Ya kuma kara da cewa makaratar lafiyar da za’a bude a karamar humar Tofa zata kasance wani sashi na bangaren makarantar nazarin fasahar lafia ta kano, School of Health Technology.
Yayin da makarantar ta ƙaramar hukumar Tsanyawa, zata kasan ce wani sashi na School of Hygiene.
Dr Bello Dalhatu shugaban makarantar kimiyya da Fasaha anan kano, yace samar da wannan cigaban zai kawo babban nasara a bangaren koyon kiwon lafiya.
You must be logged in to post a comment Login