Labarai
Kano ce ta biyu a yawan masu shaye-shaye- NDLEA

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta bayyana Kano a matsayin jiha ta biyu a matsayin jahohin Najeriya da ke da yawan masu tu’ammali da miyagun kwayoyi.
Shugaban hukumar Birgediya Janar Buba Marwa Mai ritaya ne ya bayyana hakan da yammacin ranar asabar lokacin da ya ke bude wasu gidaje da cibiyar gyaran halin masu tu’ammali da miyagun kwayoyi a barikin hukumar a shalkwatar ta da ake Kano.
Buba Marwa, ya kuma kara da cewar dole ne sai iyaye sun kara kula da yaran su tare da neman kayan gwajin kwaya don gano matsalar da daukar mataki cikin gagawa.
You must be logged in to post a comment Login