Connect with us

Labarai

Kano: Hisbah ta magantu kan rikicin ƴan adaidaita

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi kira ga al’ummar jihar musamman matasa da su guji tayar da zaune tsaye.

Babban Kwamandan hukumar Malam Haruna Ibn Sina ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran hukumar Malam Lawan Ibrahim Fagge ya fitar a daren jiya Litinin.

Malam Ibn Sina ya ce, baki-ɗaya an gina addinin musulunci ne a bisa zaman lafiya.

A don haka ya roƙi al’ummar Kano da su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da ɗorewar zaman lafiya.

Malam Ibn Sina ya kuma roƙi al’ummar Kano da su ƙara dage wa da addu’ar neman zama lafiya a jihar da ƙasa baki-ɗaya.

Wannan dai na zuwa ne bayan samun rahoton tarzoma a wasu yankunan Kano sanadiyyar zanga-zangar masu adaidaita sahu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,482 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!