Addini
Kano: Hukumar Shari’a ta ƙaddamar da kwamitoci 80

Hukumar Shari’a ta jihar Kano, ta ƙaddamar da kwamitoci guda Takwas, na malamai waɗanda za su rinƙa ziyartar hukumomi da makarantu da kuma kasuwanni, da sauran wurare, domin faɗakar da al’umma a ɓangarori daban-daban.
Kwamitocin sun haɗar da kwamitin da zai rinƙa zuwa hedikwatar Ƴan sandan Kano, da na Kasuwanni, da makarantu, da kuma na tashoshin Mota, da gidajen gyaran hali, da dai sauransu, domin faɗakar da al’umma, da ma mazauna gidaje, da makarantun.
Shugaban hukumar Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ne ya jagoranci ƙaddamar da kwamitocin a jiya Litinin a ofishin hukumar, inda ya ce kafa kwamitocin ya biyo bayan yadda suka lura da buƙatar hakan, bisa ziyarar da hukumar ta kai hukumomi da kuma gidajen a baya, inda shugabannin wuraren suka bukaci hakan domin faɗakarwa, da ilimantar da al’umma.
Sheikh Abbas Daneji, ya kuma buƙaci kwamitocin da su tsaya tsayin daka wajen gudanar da aiki yadda ya kamata, domin faɗakar da al’umma, da wa’azantar wa, tare da gyaran tarbiyya a matakai daban-daban.
You must be logged in to post a comment Login