Labarai
Kano: Jami’an Hisbah sun cafke wadanda ake zargi da yin safarar Mata

Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta ce, ta gano wasu Mata da ake zargin ana ƙoƙarin yin safararsu zuwa wasu ƙasashe domin neman kuɗi.
Mataimakin babban Kwamandan hukumar Dakta Mujahiddin Aminuddeen, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aiko wa Freedom Radio.
Dakta Mujahiddin ya ce, hukumar ta ɗauki matakin gaggawa domin hana aukuwar lamarin tare da tabbatar da cewa, an tsare lafiyarsu, domin kariya daga fadawa cikin haɗarin cin zarafi ko bautar da su.
You must be logged in to post a comment Login