Labarai
Kano: Kotu ta janye umarnin cafke jami’in Customs
Wata babbar Kotun Shari’ar Musulunci a jihar Kano, a ranar ta janye umarnin da ta bayar na kamo mata wani babban jami’in hukumar Kwastam Yusuf Ismail Mai Biscuit, da ta bayar a ranar Alhamis ɗin da ta gabata 4 ga Janairu mn bana.
Kotun ta janye wannan umarni ne ranar Juma’a kwana guda bayan bada umarnin cafke shi.
A ranar Alhamis ɗin ne Alƙalin kotun Garba Hamza Malafa ya bayar da sammacin kama Yusuf Ismail Mai Biscuit, wanda ake ƙara, sai dai, gaza amsa kiran da kotun ta yi masa ne ranar bayan fara sauraron shari’ar ta sa Alƙalin bayar da umarnin.
Sai dai a wata sabuwar odar da ta bayar mai ɗauke da sanya hannun babbar kotun shari’a a ranar Juma’a, ta ce an janye umarnin na farko ba tare da bata lokaci ba.
Kotun ta ce, janyewar ta biyo bayan bayanin lauyan da ke kare jami’in Kwastam din Barista Sani Idris wanda ya tabbatar da cewa, duk da cewa ba a kai wa wanda yake karewa sammacin ba, amma ya halarci kotun.
Da ya ke yin ƙarin haske ga jaridar Solacebase, Barista Sani Idris, ya ce, an yaudari alkalin ne a lokacin da ya je domin wakiltar wanda ya ke karewa a kan lamarin yayin da alkalin ya gudanar da shari’ar a ofishinsa.
“Muna cikin harabar kotu muna sa ran kotu za ta zauna, amma abin mamaki, an yi zaman shari’ar ne a ofishin alkali, sai aka yaudare shi da cewa ba mu zo ba.
Barista Sani ya ci gaba da cewa, ”Wanda nake karewa cikakken mutum ne mai kishin kasa, don haka ya umarce ni da in tsaya masa a kotu duk da cewa ba a kai masa sammacin kotun ba.”
Daga bisani Kotu ta sanya ranar 8 ga watan Janairu domin gabatar da ƙarar.
You must be logged in to post a comment Login