Labarai
Kano: Kwamishina ya janye daga yin belin wanda ake zargi da siyar da ƙwayoyi

Kwamishinan Sufuri na jihar Kano, Alhaji Ibrahim Namadi, ya janye daga yunƙurinsa na karɓar belin wani da ake zargi da laifin dillalancin miyagun ƙwayoyi Suleiman Danwawu, a wata shari’ar da ake yi a gaban babbar kotun tarayya da ke Kano.
Shari’ar tsakanin gwamnatin Tarayya da Sulaiman Aminu mai lamba (FHC/KN/CR/93/2025), ta shafi zargin aikata laifukan da suka shafi muggan kwayoyi.
Rahotonni sun bayyana cewa, a baya Kwamishina Ibrahim Namadi ya tsaya a matsayin wanda zai tsaya wa wanda ake tuhuma.
Sai dai a daren yau Juma’a ne Ibrahim Namadi ya sanar da janye kansa daga karɓar belin ta cikin wata wasika da ya miƙa wa mataimakin magatakardar kotun.
A cikin wasikar, Kwamishinan ya kawo dalilai na ƙashin kansa, tare da buƙatar kare mutuncinsa da kuma kare martabar ofishinsa a matsayinsa na jami’in gwamnati.
Haka kuma, ya bayyana cewa ya yanke shawarar fara zama a matsayin wanda zai tsaya masa ne bisa ga ra’ayinsa, saboda alaka ta iyali da ta dade da kuma kula da jin kai.
You must be logged in to post a comment Login