Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

EFCC ta gurfanar da Wani gaban Kotun a Kano

Published

on

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta gurfanar da Umar Bello Sadiq a gaban babbar kotun jihar Kano, karkashin mai shari’a Zuwaira Yusuf bisa zargin sa da laifukan damfara.

An gurfanar da Umar Bello ne tare da kamfaninsa Marula Global Links bisa zargin karbar naira miliyan 20 daga hannun mai dakin mai martaba Sarkin Bichi, Farida Nasir Ado Bayero da sunan zuba jari a fannin ma’adanai, inda daga bisani ya karkatar da kudaden.

Lauyan masu gabatar da kara, Sadiq Kurawa ya bukaci kotun da ta sanya ranar fara sauraren shari’ar, yayin da lauyan wanda ake zargi ya bukaci kotun ta bada belin wanda yake karewa.

Mai shari’a Zuwaira Yusuf ta amince da bada belin wanda ake kara kan kudi naira dubu dari biyar tare da mutane biyu da zasu tsaya masa daga ‘yan uwansa na jinni, tare da sanya ranar 24 ga watan Nuwanba domin fara sauraren karar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!