Labarai
Kano: Ma’aikatar Muhalli ta ƙaddamar da kundin dokokin da ta fassara zuwa Hausa

Ma’aikatar Muhalli da Sauyin yanayi ta jihar Kano, ta ƙaddamar da kundin dokokin tsaftar muhalli da ta fassara su daga harshen Turanci zuwa Hausa.
Kwamishinan ma’aikatar, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a Larabar makon nan.
Ya ce, an fassara kundin dokoki da kuma kundin ƙa’idojin kula da gurɓatar muhalli ne domin sauƙaƙawa wajen fahimta da kuma ci gaba da wayar da kan jama’a a kan dokokin tsaftar muhalli
Dakta Dahir Muhammad Hashim, ya kuma bayyana cewa, tun a watan Afrilun da ya gabata ne ya ɗauki alƙawari ncewa za a fassara dokokin zuwa harshen Hausa.
You must be logged in to post a comment Login