Connect with us

Labarai

Dan jihar Kano ya fassara littafin Sahihul Bukhari zuwa Hausa

Published

on

Wani malamin addinin musulunci a Kano Dakta Aminu Isma’il Abdulkadir ya ce yanzu haka ya samu nasarar kammala fassara littafin Sahihul Bukhari zuwa harshen Hausa.

Cikin wani sako da shehin malamin ya wallafa a shafinsa na Facebook ya yi godiya ga Allah sannan ya ce ya samu ikon Allah ya samu ikon kammala fassara wannan bayan ya shafe tsawon shekaru takwas yana wannan aiki.

Dakta Aminu Isma’il ya ce fatansa shi ne littafin ya amfani al’umma.

Dakta Aminu Isma’il Abdulkadir

Al’umma da dama dai sun ta bayyana ra’ayoyinsu tare da jinjina ga malamin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!