Labarai
Kano: Matashi ya rasu sakamakon nutsewa a Kududdufi

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, tabbatar da mutuwar wani matashi mai suna Sulaiman Nura Ado, mai kimanin shekaru 14, sakamakon nutsewar da ya yi a cikin wani kududdufi da ake kira da Ruwan Promise da ke unguwar Rijiyar Zaki.
Ta cikin wani sakon murya da ya fitar ga manema labarai, mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya ce, sun samu kiran gaggawa ne bayan afkuwar lamarin.
Ya ce, jami’an hukumar sun samu nasarra ciro matashin daga cikin ruwan kafin rasuwarsa.
ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya ce, iftila’in ya faru ne a karshen makon da mu ka yi bankwana da shi.
Hukumar ta bukaci iyaye da sauran al’umma da su guji barin yara su na yin wanka a irin wadannan kududdufai domin kauce wa irin wannan iftila’i.
You must be logged in to post a comment Login