Labarai
Tattalin arzikin Najeriya ya fara farfadowa daga matsalolin da ya fuskanta
Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Wale Edun, ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya, ya fara farfadowa daga matsalolin da ya fuskanta a baya.
Wale Edun, ya ce, lokacin da shugaba Bola Tinubu, ya hau mulki a 2023, tattalin arzikin na gab da durƙushewa, amma yanzu an samu ci gaba, inda ma’aunin tattalin arzikin kasa na GDP ya ƙaru da kashi 4.23 cikin ɗari, hauhawar farashin kaya ta sauka zuwa 18.02 cikin ɗari.
Ya kara da cewa darajar naira ta ƙaru zuwa N1,457 kan kowace Dalar Amurka, kuma farashin abinci kamar buhun shinkafa ya sauka daga N120,000 zuwa kusan N80,000.
Ministan ya kuma amince cewa har yanzu akwai ƙalubale, musamman wajen biyan bashin ƙasa da ƙarancin kuɗin shiga, amma ya ce, sabuwar dokar haraji da sauran matakan da gwamnati ke ɗauka za su ƙara ƙarfin tattalin arzikin.
Haka kuma, Ministan, ya kara da cewa burin gwamnatin shugaba Tinubu shi ne kai ci gaban tattalin arziki zuwa kashi bakwai cikin ɗari nan da shekarar 2027.

You must be logged in to post a comment Login