Connect with us

Labaran Wasanni

Kano Pillars za ta dawo filin wasanta na Ƙofar Mata – LMC

Published

on

Hukumar shirya gasar cin kofin kwallon kafar firimiya ta Najeriya LMC ta ce Kano Pillars za ta ci gaba da wasa a filin wasan ta na Sani Abacha dake kofar Mata.

Babban Jami’i a hukumar Alhaji Salihu Abubakar ne ya bayyana hakan yayin ziyarar da suka kawo nan Kano a ranar Asabar 23 ga watan Oktoban da muke ciki ta 2021, domin duba halin da filin wasan yake ciki domin tunkarar gasar wasannin ta shekarar 2021/2021.

Alhaji Salihu Abubakar ya ce “Kano Pillars za ta ci gaba da wasannin ta na Firimiya a watan Nuwambar shekarar da muke ciki ta 2021″.

Ya kuma ce, “a zagayen da mukayi cikin filin wasan mun gamsu da yadda aka gudanar da gyare-gyare a cikinsa”.

Ya kuma ce dawowar Kano Pillars Kano domin ci gaba da wasannin ta zai taimakawa kungiyar da kuma gasar duba da yawan magoya bayan da Pillars din take dashi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!