Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: Rundunar ƴan sanda ta bai wa iyalan jami’an ta da suka rasu tallafi

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bai wa iyalan wasu jami’an ta biyu da suka rasu a bakin aiki tallafin naira miliyan ɗaya da dubu dari biyu da hamsin don rage musu radadi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.

Sanarwar ta ce, kwamishinan ‘yan sanda Samaila Shuaibu Dikko ya miƙawa iyalan jami’an kudaden a karkashin shirin biyan iyalan wadanda suka rasu a bakin aiki inshora, wanda Sifeton ‘yan sandan kasar nan ke jagoranta.

Samaila Shuaibu Dikko ya kuma gargadi ‘yan uwan mamatan da suyi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace, musamman wajen tallafawa marayun da aka bar musu da kuma ‘yan uwansu domin rage musu radadi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!