Labarai
Kano: Rundunar yan sanda ta gargadi masu bai wa yara baburan Adaidaita Sahu

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta gargadi mamallaka baburan Adaidaita sahu kan su guje wa bai wa kananan yara baburan suna hawa kan titunan jihar tare da gudanar da sana’a da su.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan SP Abdullahi Hauna Kiyawa, ne ya bayyana hakan A daren Litinin din makon nan.
SP Kiyawa, ya ce, a cikin watannan da muke ciki na Agusta kadai yaran da ke tuka irin wadannan babura na Adaidaita sahu sun haddasa hadura har guda goma sha shida.
Ya yara da cewa, rundunar ta shirya tsaf don ganin ta cafke tare da gurfanar da duk wanda aka samu da aikata wannan laifi.
Haka kuma ya gargadi masu tukin ganganci da kuma masu kin bin dokar fitilar bada hannu da su guji yin hakan ko kuma su fuskanci fushin hukuma.
You must be logged in to post a comment Login