Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rundunar ‘yan sandan Kano ta kama matasan da suka fake da tashe suna kwacen wayoyi

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Kano ta kama wasu matasa sama da ashirin da ta ce suna fashin wayoyin jama’a.

 

A cewar rundunar matasan sun fake da tashe ne suna fashi wa jama’a.

 

Mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa matasan dauke da muggan makamai sun fito ne daga sassa daban daban na Kano suna gudanar da al’adar nan ta tashe, inda daga bisani suka sauya akalarsa zuwa kwacen wayoyin mutane da karfin tsiya.

 

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, bayan kwacen wayoyin matasan suna kuma saran jama’a da wukake da adduna sannan su karbe musu duk kayayyakin da ke hannunsu.

 

Haka zalika rundunar ta kuma kama masu fadan daba da masu satar wayoyin hannu a cikin baburan adaidaita sahu

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!