Connect with us

Labarai

Kano: Yara 2 sun rasu sakamakon nutsewa a kududdufi garin Najauro

Published

on

Wasu yara biyu sun rasu sakamakon nutsewa a wani kududdufi da ke yankin Najauro a Karamar Hukumar Dawakin Kudu ta jihar Kano.

 

Rahotonni sun ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a wani kududdufi da ke kofar arewa kan hanyar zuwa babban asibitin Dawakin Kudu yayin da yaran suka je domin yin wanka inda suka nutse a ciki.

 

Al’ummar unguwar sun yi kokarin lalubo gawarwakin yaran, inda aka samu daya nan take.

 

An kuma ɗauki lokaci kafin a samo dayan, da taimakon ɗan gidan Sarkin Ruwa mai suna Dan Babiyo Jarmai inda aka samu nasarar fito da gawar daya yaron.

 

Yaran da suka rasu sun hada da Naziru Saleh mai shekaru 11 da Mubasshir Sani mai shekaru 12.

 

Tuni aka yi jana’izarsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!