Labaran Kano
KANO: Yara fiye da miliyan 3 za su karbi allurar riga-kafin shan inna
Gwamnatin Kano ta ce burinta akan digon riga kafi a yanzu shine ta yiwa akalla yara fiye da miliyan uku digon allurar cutar shan inna a kananan hukumomin 44 da ke fadin jihar kano.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana haka ne a makon da ya gabata a yayin bikin digon allurar riga-kafin shan inna ga yara da yan gudun hijira, wanda aka gudanar a asibitin kauye dake karamar hukumar Kabo.
Gwamna Ganduje wanda kwamsihinan lafiya Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa ya wakilta ya ce gwamnatin Kano ta dage wajen tabbatar da an kawar da cutar shan inna a jihar Kano.
Ya kara da cewa sama da shekaru biu da suka gabata jihar kano bata samu bullar shan inna a jikin kowanne yaro ba, kamar yadda jami’n hulda da jama’a na ma’aikatar Ismail Garba Gwammaja ya bayyana.
Ya kuma yaba da irin gudunmuwar da kungiyoyin da suke tallafawa ma’aikatar lafiya wajen kawar da wanann cuta, musammam a bangaren riga kafi da cutar zazzabin cizon sauro da cuta mai karya garkuwa.
Da yake jawabi shugaban hukumar lafiya ta bai daya Dr Tijjani Hussain ya bukaci shugabanin gargajiya da malaman addini su rika taimakawa wajen wayar da kan alummarsu don karbar digon allurar riga kafin cutar shan inna.