Labarai
Karamar Hukumar Shanono ta bukaci gwamnati ta gyara Dam ɗin yankin tare da gina wani sabo

Shugaban karamar hukumar Shanono, Alhaji Abubakar Barau, ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta gina sabon Dam a garin Dutse da kuma gyara Dam ɗin Shanono, domin sauƙaƙa matsalar ruwa da ake fama da ita a yankin.
Abubakar Barau, Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Kwamishinan ma’aikatar raya karkara Dakta Abdulkadir Abdussalam, a ofishinsa, inda ya ce, al’ummar ƙaramar hukumar na matukar shan wahala wajen samun ruwan da za su yi amfani da shi.
A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar, Faruk Ghali Masanawa ya fitar, shugaban ƙaramar hukumar ya gode wa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, da Kwamishinan raya karkara bisa ziyarar da suka kai domin jin koken jama’a a karkara.
Kwamishina Abdussalam, wanda ya samu wakilcin Babban Sakataren ma’aikatar, Alhaji Musbahu Ahmad Badawi, ya ce, ziyarar na cikin matakin tattara bayanai domin samar da ababen more rayuwa a kananan hukumomi.
You must be logged in to post a comment Login