Labarai
Karamarn hukumar Dala ta haramta yin wasannin bukukuwa da kidan Gangi

Shugabancin Karamar Hukumar Dala, ya haramta duk wani wasa a lokacin bukukuwan aure, da kuma kidan gangi a fadin karamar hukumar, sakamakon yadda wasu ke fakewa da hakan suna tayar da hankalin jama’a.
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da aka samu wasu bata-gari da aka hana su yin wasan kauraye na kidan gangi a unguwar Rijiya Biyu dake karamar hukumar, inda daga bisani suka dawo cikin dare suka kunna wuta a gidan Mai Unguwar yankin.
Da yake bayyana irin matakin da shugabancin karamar hukumar zai dauka, Shugaban Karamar Hukumar ta Dala, Suraj Ibrahim Imam, ya ce ba za su saurara wa duk wanda aka samu da hannu a cikin wannan al’amari ba.
Ya kuma bukaci al’umma da su ba wa karamar hukumar cikakken hadin kai domin ganin hakan bai sake faruwa ba a nan gaba ba.
You must be logged in to post a comment Login