Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

KARANCIN MANIYYATA AIKIN HAJI DAGA NAJERIYA

Published

on

Tun daga shekarar 2017 ne adadin maniyyata aikin haji ya ke raguwa a Najeriya, wannan kuwa za a iya cewa ya samo asali ne sakamakon tashin gwauron zabin da kujerun aikin haji su ka yi.

Wanda hakan ya biyo bayan dagawar farashin dalar Amuruka a kan naira har sau dari uku da biyar (N305) a farashin babban bankin kasa wato CBN.

Idan mu ka duba shekarun baya alal misali daga shekarar 2008 zuwa 2015, maniyata aikin haji na fuskantar babban kalubale kafin su samu damar iya mallakar kujerar aikin haji.

A wannan lokacin sai miniyaci na da hanya mai karfi ko kuma masu gidan rana sun zagaya a tsakanin miniyaci da jami’in hukumar alhazai, ko kuma a samu sa’ar cin kuri’a wadda a ke yiwa maniyata a kananan hukumomi wato Gida ko Makka, idan maniyaci yai dacen daukar Makka to ya samu damar shiga sahun mahajjatan wannan shekarar, har a fara taya shi murna. Wanda kuma bai samu sa’a ba hannunsa ya dakko gida to ya fita daga sahun mahajjata, saidai yawan rai wato badi ko kuma ya sauya tinani ya bi ta gajeriyar hanya.

Wato a fa wancan lokacin kasar Saudi Arabia na bawa kasar nan adadin kijerun aikin haji har kusan duba dari (10,000) saidai a wajejen 2011 zuwa 2017 an rage yawan kujerun sakamakon aikin fadada masallacin Harami dake Makka.

Amma duk da yawan kujerun masu bukata sun fi su yawa sosai.

An fara samun raguwar maniyata ne a shekarar 2017 bayan da hakikanin farashin kujerar aikin haji ya fito daga bakin masu ruwa da tsaki har sama da naira miliyan daya da rabi, to a nan ne fa maniyyata su ka fara nuna gazawa wajen kasa cika kudin kujerun da su ka biya wa kudin na gani ina so.

Amma za a iya cewa an samu yawan alhazai a shekarar domin sun tsallake dubu hamsin wadanda su ka sauke farali, amma wadanda ba su iya cika kudinsu ba hukumomin alhazai sun mayar masu da kudadensu bayan an dawo daga kasa mai tsarki, inda wasu kuwa su kar kudinsu a asusun humomin alhazan da zummar badi su cika dan ganin sun sauke wannan ibada.

Abun mamaki a shekar 2018 ita shekara mafi muni a karancin maniyata domin duka-duka mahajjata n da su ka hallaci aikin Hajji daga nan Najeriya ba su fi dubu ashirin da biyu zuwa da biyar ba a duk fadin kasar.

A halin yanzu hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta tsayar ta ranar 10/7/2019 dan fara jigilar maniyata zuwa kasa mai tsarki, saidai har yanzu kofa na bude dan cigaba da biyan kudin aikin haji.

Ko a kwana-kwanan nan hukumar alhazai NAHCON, ta kara wa’adin lokacin rufe karbar kudin kujerun aikin haji har zuwa 15/7/2019 sabanin shekarun baya.

Abunda har yanzu hukumomin alhazan su ka kasa sanarwa manema labari shi ne adadin maniyatan da su kai rijista du su, in banda hukumar alhazan jihar Kaduna da ta sanar da cewa sama da maniyata 3000 sun gama biyan kudaden kujerunsu. Amma sauran jihohin kuwa shiru ka ke ji kamar malam ya ci shirwa.

Ko a bara ma jihar Kaduna ita ce ta fi kowacce jiha yawan alhazan da su ka sauke farali a shiyar arewa maso yamma, wanda a baya jihar Kano ce ke daukar kambi a yawan alhazai a duk fadin Najeriya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!