Connect with us

Labarai

RUKUNIN FARKO NA MA’AIKATAN HUKUMAR ALHAZAN NAJERIYA NAHCON SUN ISA KASA MAI TSARKI DAN FARA KARBAR MANIYATA AIKIN HAJIN BANA.

Published

on

A yau Juma’a 5/7/2019 tawagar farko ta ma’aikatan hukumar alhazan Najeriya NAHCON su ka bar gida zuwa kasar Saudi Arabia, dan fara karbar maniyata aikin hajin bana na kasar.A ranar Laraba 10 ga watan Juli ne a ke sa ran fara jigilar maniyata aikin hajin bana daga nan gida Najeriya zuwa kasa mai tsarki. A wannan shekara dai za a bude aikin jigilar ne a jihar Katsina da maniyatan jihar.A lokacin da ya ke bankwana da jami’an shugaban hukumar alhazan Najeriya NAHCON Barr Abdullahi Mukhtar ya hore su da su tabbatar sun sauke hakkin da ke kansu wanda shi ne dalilin zuwan su kasa mai tsarkidan kulawa da alhazai bakin Allah.A bara dai an fara jigilar ne a birnin Tarayya Abuja da maniyatan na Abuja, a na sa ran fara jigilar Maniyata aikin haji daga jihar Kano, a ranar Alhamis 11 ga watan Julin nan idan Allah Ya kai mu, kamar yadda jami’in hukumar alhazan Najeriya NAHCON mai kula da shiyar Arewa maso Yamma Alhaji Lawan Ahmad Katsina ya shekada mana a ganawar sa da ‘yan kungiyar Kano Hajj Reporters Forum a ofishinsa da ke Kano.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!