Connect with us

Labarai

Karin Farashi : Buhari ya kara wa’adin mako guda

Published

on

Gwamnatin tarayya ta kara wa’adin dakatar da sabon farashin kudin wuta da akalla mako guda.

Shugaban hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta kasa Farfesa James Momoh ne ya bayyana haka, bayan kammala taro da gamayyar kungiyoyin kwadagon kasar nan da safiyar yau a Abuja.

Tun farko dai gwamnatin ta dakatar da sabon farashin kudin wutar lantarkin ne na makwanni biyu wanda wa’adin yazo karshe a daren jiya Lahadi goma sha daya ga watan da muke ciki.

Ya ce kara wa’adin dakatar da karin farashin kudin wutar lantarkin zai taimaka gaya wajen bai wa hukumar da ‘yan kwadago damar nazartar hanyoyin da za a bi kafin fara amfani da shi.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,993 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!