Connect with us

Kaduna

Ta’addanci : ‘yan bindiga sun hallaka mutane 9 a Kaduna

Published

on

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun hallaka mutane tara a kauyen Kadai a karamar hukumar Giwa, a wanni kadan bayan da suka kai wani maakamancin wannan hari a garin Kidandan inda suka hallaka mutane shida.

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda ake zargin sun shiga kauyen da misalin karfe tara na safe, inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansanda a jihar ta Kaduna ASP Muhammad Jalige ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ta cikin wata sanarwar da ya fitar.

Ta cikin sanarwar Muhammad Jalige ya ce, gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El’rufa’I, ya mika sakon jaje ga mazauna Kauyukan da lamarin ya faru.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,993 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!