Labaran Kano
Karin kudaden haraji da gwamnati tayi ka iya durkusar da masana’antu- MAN
Kungiyar masu masana’antu ta kasa MAN ta bayyana cewar karin kudaden haraji da gwamnati ta yi a yan kwanakin nan na iya haddasa barazanar durkushewar masana’antu a kasar nan.
Shugaban kungiyar reshen jihar Kano Alhaji Sani Husain Sale ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hansi na nan Freedom Radiyo da aka gudanar a safiyar yau talata.
Alhaji Sani Husain ya kurma kara da cewar karin kudin zai janyo matsaloli da dama ta bangaran kasuwanci, wanda a yanzu haka ma sun fara samun karancin abokan cinikayya.
A na sa bangaren shugaban Kwamitin dattawa da masu ruwa da tsaki na kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi da aka fi sani da kasuwar Sabon Gari Alhaji Ibrahim Danyaro, ya bayyana cewar idan har gwamnati za ta tafiyar da kudaden harajin domin amfanar da al’ummar kasa, hakika hakan zai saukakawa al’umma radadin da suke ciki a yanzu.
Bakin sun kuma bukaci gwamnati da ta kasance mai tuntubar masaana kafin zartar da duk wani kudirinta.