Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Karin kudin makarantun Jami’o’i barazana ce ga harkokin tsaro: SEDSAC

Published

on

  • Mata sa zasu iya shiga matsala sakamakon karin kudin makaranta.
  • Da gwamnatin tarayya tasan matsalar da karin kudin nan zai jawowa kasar nan da bata yi buris da bukatun ASUU ba.
  • Kafin a kara kudin makarantar ma wasu daliban basa iya biyan kudin makarantar.

Wani mai fashin baki kan al’amuran yau da kullum dake jihar Kano, kuma shugaban kungiyar SEDSAC mai rajin habbaka harkokin ilimi kwamred Umar Hamisu Kofar Na’isa ya ce, karin kudin makarantar da jami’o’i suka yi ba karamar barazana zai haifarwa kasar nan ba, musamman a bangaren matasa.

Kwamred Umar Hamisu Kofar Na’isa ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da wakiliyar Freedom Radio Shamsiyya Farouk Bello.

Wanda yace ‘da gwamnatin tarayya tasan irin illar da karin kudin makarantar nan zai jawowa daliban kasar nan, da bata ki biyawa malaman jami’o’i bukatunsu ba’.

Kwamret Umar Hamisu Kofar Na’isa ya kara da cewa ‘ tun kafin a kara kudin makarantun jami’a, wasu daliban basa iya biyan kudin makarantar, wanda karinsa a yanzu zai kara sawa matasan kasa cigaba da karatun’.

A hannu guda shugaban kungiyar malaman Jami’o’i na Jihar Kano Farfesa Abdulkadir Muhammad cewa yayi ‘wannan matsalar na daya daga ciki abubuwan da malaman jami’a suka guda, wanda ya haddasa musu tafiya yajin aikin da sukayi na tsayin watanni takwas’.

Farfesa Abdulkadir Muhammad ya kuma ce ‘wannan ‘yan kare karen da akayi a yanzu ma ba komai bane fyace kudin irin nasu jarabawa dana magunguna da sauran su, nan gaba ma kudaden zai tashi daga dubu dari biyu, zuwa dubu dari bakwai koma sama da haka’.

Don haka suke fatan gwamnati zatayi abinda ya kamata, don ganin talaka ya samu ilimi kamar kowanne dan kasa.

 

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!