Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kwana guda bayan soja ya harbe direba: Direbobin Tirela sun ki amincewa su bude hanyar Kano zuwa Zaria

Published

on

Har zuwa yammacin yau Juma’a, direbobin manyan motoci sun tsare  hanyar Kano zuwa Zaria, tare da kin amincewa su janye daga kudirinsu na sai an biya su hakkin kisan ‘dan uwansu da ake zargin wani soja da yi.

Dan uwan mamacin ya ce bazasu bude hanyar ba har sai an biya musu bukatarsu.

A jiya ne dai  direbobin suke ikirarin wani jami’in soji ya harbe dan uwansu a wani shinge a kan hanyar.

Har yanzu direbobin tirela da suka rufe hanyar Kaduna Zuwa Kano na nan a kan kudurinsu, na kin bude hanya har sai an biya su diyyar dan uwansu da wani soja ya kashe.

Freedom Radio ta sake tuntubar dan Uwan Marigayi sake tuntubar su kan halin da ake ciki a yau.

Yusuf Habibu Usman ya ce, ‘suna nan a kan bakansu na kin bude hanyar har sai an biya su diyar naira Miliyan Sittin.

A jiya ne dai muka kawo muku rahoton yadda direbobin tirelar suka yi zaman dirshen a babbar hanyar Kaduna Zuwa Kano tare da rufe ta, suna ikirarin cewa sai an biya su diyyar dan uwansu da wani soja ya kashe sannan za su bude ta.

Rahoton: Halima Wada Sinkin

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!