Labarai
Karo Na Biyu:Gwamnan Kano Abba Gida-Gida ya ƙaddamar da rabon kayan Abinci
Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da rabon kayan abinci karo na biyu ga al’ummar jihar na ƙananan hukumomi 44, inda gwamnatin ta ce zata fara rabawa al’ummar kano ta tsakiya adadin buhhuna 105600 da suka haɗar da shinkafa da masara
Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya tabbatar da hakan a yau yayin taron ƙaddamar da rabon kayan abinci ga al’umma jihar Kano domin rage matsin rayuwa da al’umma suke ciki
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma ce zasu kasance masu saka ido wajen ganin kayan sun isa ga mabuƙatu a dukkanin ƙananan hukumomi kano
Gwamnan ya kuma ƙara da cewa sunyi tsarin zuwa gidan marayu da gajiyayyu da sauran guraren da su ke a killace domin basu nasu kayan abincin
Haka kuma gwamnan ya ce suma dukkan wani nau’i na jami’an tsaro da ƴan jarida suma akwai wani tsari da akayi musu wajen suma wannan kayan abincin sun isa gare su
A karo na biyu gwamnatin zata raba sama da buhhuna sama da dubu ɗari a wannan lokaci inda tace zata ci gaba da samarwa da al’ummar jihar hanyoyin samar musu da saukin rayuwa
You must be logged in to post a comment Login