Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Karon farko Aisha Buhari ta magantu kan matsalar sace dalibai

Published

on

Mai dakin shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari ta koka kan yadda ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram ke ci gaba da sace mata da kuma dalibai suna garkuwa da su a kasar nan musamman a yankin arewa.

Hajiya Aisha Buhari ta wallafa wannan jawabi ne a shafinta tiwita, domin bikin tunawa da ranar mata ta duniya da ake gudanarwa a yau, inda ta ce a matsayinta na uwa, tana jimamin halin da wadanda ifti’la’in ya fadawa da ma iyalansu suke shiga.

Ta kuma bukaci masu ruwa da tsaki da su yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen sace-sacen jam’a da garkuwa da ake ci gaba da yi a kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!