Labaran Wasanni
Karon farko cikin shekaru 16 za a buga El-Clasico babu Messi da Ronaldo
A yau Lahadi 24 ga Oktoban shekarar 2021 da muke ciki za’a buga wasan hamayya mafi kayatarwa a duniya tsakanin Barcelona da kuma Real Madrid karawar da akaiwa take da El-Clasico.
Wasan dai zai gudana a filin Camp Nou Mallakin Barcelona.
Sai dai wasan zai gudana akaron farko bata reda ‘yan wasa Lionel Messi na Barcelona ba da kuma Cristiano Ronaldo tin daga shekarar 2005.
Dan wasa Messi dai ya fara buga wasan El Clasico ne a ranar 19 ga watan Nuwambar shekarar 2005 da Real Madrid tayi nasara a filin wasanta na Estadio Santiago Bernabeu daci 3-0 akan Barcelona.
Sai dai tin bayan fara buga wasanni da ‘yan wasa Messi da Ronaldo sukai sun samu nasarar zura kwallaye da dama.
Inda Lionel Messi ya buga wasani 45 ya kuma zura kwallo 26 a Barcelona.
Yayin da Cristiano Ronaldo ya buga wasanni 30 ya kuma zura kwallaye 18 a wasan hammaya na El Clasico.
Wannan karon ana gani dama ce ga dan wasan Karim Benzema da zai cigaba haskawa musamman yadda shine dan wasa daya tilo mai yawan shekaru da zai buga wasan tsakanin ‘yan gaban duka kungiyoyin guda biyu.
Real Madrid dai zata fukanci Barcelona da ‘yan wasa kamar haka
Masu tsaran gida Courtois, Lunin da Luis López.
Sai ‘yan wasan baya Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Marcelo da Mendy.
Akwai ‘yan wasa tsakiya kuma Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., Camavinga da Blanco.
Sai kuma ‘yan wasan gaba da suka hada da Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da Mariano.
A gefe guda kuma ‘yan irinsu Gareth Bale, Isco, Luka Jovic Dani Ceballos ba zasu fafata a wasan ba samakon jinyar rauni da suke fama da shi.
Daga bangaren Barcelona kuma akwai masu tsaran gida Marc-André ter Stegen Neto da Iñaki Peña
Da ‘yan wasan baya Sergiño Dest, Gerard Piqué, Clément Lenglet, Jordi Alba, Óscar Mingueza, Samuel Umtiti, Eric García, da Alejandro Balde
‘Yan wasan tsakiya kuma akwai Sergio Busquets, Riqui Puig, Yusuf Demir, Philippe Coutinho, Sergi Roberto, Frenkie De Jong, Nico González, da kuma Gavi
Yayinda ‘yan wasan gaba kuma suka hada da Memphis Depay, Ansu Fati, Luuk De Jong, da Sergio Agüero.
Wasan karshe da suka buga tsakaninsu a ranar goma ga watan Afrikun shekarar da muke ciki Real Madrid tayi nasara akan Barcelona da ci 2 da 1.
You must be logged in to post a comment Login