Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

KAROTA ta kama mutane 5 da sukewa hukumar sojan gona

Published

on

Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jihar Kano KAROTA ta sami nasarar cafke wasu matasa biyar suna sojojan gona da hukumar.

Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka a yau ta cikin wata sanarwa da Kakakin Hukumar ta KAROTA Nabilusi Abubakar Kofar Nai’sa ya sanya wa hannu

Ya Kuma bayyana cewa ‘an jima ana kawo ƙorafi hukumar cewa jami’anta na matsawa al’umma da karɓe-karɓen kuɗi’.

‘Bayan zurfafa bincike a wannan rana an sami nasarar cafke mutum biyar daga cikin wadanda ake zargin’.

Sanarwar ta bayyana cewa ‘Shugaban Hukumar ya ce za a dauki matakin gurfanar da su a gaban ‘yan sanda domin zurfafa bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace’.

Shugaban ya Kuma roƙi al’umma da su ci gaba da bawa Hukumar KAROTA haɗin kan da ya dace domin gudanar da ayyukanta bisa tsarin doka da oda.

Rahoton:Bashir Sharfadi

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!