Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsohon Kwamishinan Ganduje ya bai wa Gwamna Abba shawara

Published

on

Tsohon kwamishinan Yada Labarai na gwamnatin Gwanduje Kwamared Muhammad Garba, ya bukaci gwamnatin Kano mai ci karkashin jagorancin Engr Abba Kabir Yusuf, da ta mayar da hankali kan samar da tsarin da zai fitar da mutanen Kano daga wahalhalun rayuwa da suke fuskanta, ba kushe ga tsarin da gwamnatin tarayya ta bujiro da shi na rabon kayayyakin tallafin rage radadi ba.

Tsohon kwamishinan ya bayyana hakan ne ta cikin sanarwar da ya fitar jiya Lahadi, a matsayin martini ga furucin gwamnatin Kano a kan shirin rabon  tallafi da gwamnatin tarayya ke shirin yi.

Idan ba a manta ba mataimakin Gwamnan Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya soki tsarin da gwamnatin tarayya ta bujiro da shi wajen rabon kayayyakin tallafin rage radadin da al’umma ke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!