Labarai
Kasafin baɗi: Masari ya gabatar da Naira biliyan 340 ga majalisar dokokin jihar
Gwamna jihar Katsina Aminu Bello Masari ya gabatar da kasafin kuɗin baɗi Naira biliyan 340 ga majalisar dokokin jihar domin amincewa.
Da yake gabatar da kasafin kuɗin, Masari ya ce na baɗi ya fi na shekarar 2021 sama da Naira biliyan 48.
Ya ce kasafin ya kunshi naira biliyan 102 da ake kashewa yau da kullum, wanda ya nuna kashi 30.40 cikin 100 da kuma naira biliyan 238 da ake kashewa, wanda ya kai kashi 69.85 bisa 100.
“An tsara kasafin kudin 2022 ne don kammala ayyukan da ake gudanarwa da kuma fara wasu manyan ayyuka da za a iya kammala su kafin cikar wa’adin gwamnati na” a cewar Masari.
“Jimillar adadin da aka yi hasashen za a gudanar da kasafin kudin shekarar 2022 ya kai Naira biliyan 175 wanda ya kunshi kudaden shiga na Naira biliyan 61 daga hukumar tattara haraji ta jihar da sauran ma’aikatu.
Masari ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali ne kan inganta ayyukan raya al’umma ilimi, kiwon lafiya, albarkatun ruwa, noma, muhalli, ayyukan gidaje da sufuri.
You must be logged in to post a comment Login