Labarai
Kasafin kudin 2021 : Majalisar dokoki ta Kano zata fara yin nazari
Majalisar dokokin jihar Kano ta ce zata rarraba kudirin kasafin kudin badi da gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar mata ga kwamitocinta don bincika akwai gyara a ciki sassan da ke bukatar gyara a cikinsa.
Shugaban majalisar Alhaji Abdulaziz Garba Gafasa, ne ya bayyana jim kadan bayan da gwamnan ya gabatar da kasafin a yau Talata.
Alhaji Abdulaziz Garba Gafasa, ya ce, kundin tsarin mulkin kasa ne ya bada dammar gwamna ya gabatar da kasafi gaban zauren majalisar ita kuma ta bincika idan akwai gyara ta yi gabanin amicewa da shi.
A ganawarsa da manema labarai bayan gabatar da kasafin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya ce kasafin na bana bai kai na badi yawa ba kuma an fi baiwa bangaren ilimi muhimmanci a cikin kasafin.
A nasa bangaren Alhaji Salisu Muhammad Ibrahim mai wakiltar mutanen karamar hukumar Doguwa da ke shugabantar kwamitin bibiyar kudaden da ake kashewa a ma’aikatun gwamnati watau PAC, cewa ya yi in dai har gwamnati ta aiwatar da abubuwan da kasafin ya kunsa to tabbas za’a samu nasarori da kuma cigaba a jihar Kano.
Rubutu masu alaka
Ganduje : Abubuwa 8 da ba’a sani ba kan kudirin kasafin kudi na Kano
Ganduje ya naɗa sabon shugaban kwalejin kimiyya da fasaha ta Kano
Wakilinmu na majalisar dokokin Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito cewa, Alhaji Salisu Muhammad Ibrahim, ya kara da cewa, gwamnan ya gabatar da kasafin a dai-dai lokacin da ya dace kasancewar majalisar za ta kammala aikinsa kafin watan janairu badi.
You must be logged in to post a comment Login