Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kai Tsaye : Ganduje zai kashe fiye da Naira biliyan 147 a kasafin kudin badi

Published

on

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin sa zata kashe fiye da Naira 147,935,302,948 a kudirn kasafin kudin badi, wanda aka yi wa take da” farfado da tattalin arziki da kuma dorewar cigaban rayuwar al’umma” 

Ganduje na gabatar da kudirin kasafin kudin badin ne a kwaryar majalisar dokoki ta Kano.

Ganduje ya ce kasafin kudin badin zai maida hankali wajen baza komar tattalin arziki wajen samar da kudaden shiga da zumar kafa harsashin  cimma manufofin gwamnati mai ci.

Da yake jawabi shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano Abdulaziz Garba Gafasa ya ce majalisar zata fara yin nazari kan kudirin kasafin kudin badin wajen  yin Taza da Tsifa.

Abdul’aziz Garba Gafasa ya ce nan bada jimawa ba majalisar zata kira shugabanin ma’aikatu da hukumomi da sashi-sashi wajen kare kasafin a gaban kwamitocin majalisar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!