Connect with us

Labarai

Shugaba Donald Trump ya ce nan bada dadewa ba kasarsa zata turo da jiragen yaki

Published

on

Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce nan ba da dadewa ba kasar sa za ta turo da jiragen yakin nan da kasar nan ta saya daga Amurka akan kudi dala miliyan 496.

Donald Trump ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar White House.

Ya ce ba ko shakka jiragen za su taimakawa rundunar sojin kasar nan wajen kakkabe mayakan Boko haram.

Shugaban na Amurka ya kuma ce kasar sa za ta ci gaba da taimakawa Nigeria a yakin da take da ‘yan ta’adda da kuma harkokin da suka shafi tattalin arziki.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,481 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!