Labarai
kasashe Afrika 16 na fama da karancin abinci-Majalisar dinkin duniya
Hukumar samar da abinci da kayayykin noma na majalisar Dinkin Duniya ta ce kasashe goma sha shida na fama da karancin abinci a fadin duniya, ciki har kasashen Afrika.
Hukumar ta ce kasashen da abun ya shafa sun hada da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da Burundi da Liberia da Mali da Somalia da Sudan ta kudu da kuma Sudan.
Sauran kasahen sune Guinea-Bissau da Haiti da Iraq da Afganistan da Lebanon da Syria da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da Ukraine da Burundi da kuma kasar Yemen.
Hukumar ta ce yawaitar rikice-rikece da ake samu a kasashen shi ne umul-abaisin samun karancin abinci ga al’ummar kasashen.
A cewar ta, kasashen Yeman da Sudan ta kudu da Syria da Lebanon da Ukraine da Afganistan da kuma kasar Somalia sun samun karancin abinci.